Jami'an tsaro a jihar Agadez ta Jamhuriyar Niger na ci
gaba da tsare wani dan jarida daga Nigeria da ya je kasar
don neman labarai.
Shi dai dan jaridar mai suna Lawal Danjuma Adamu da ke
aiki a kamfanin jaridar DailyTrust a Nigeria ya je Nijar din
ne domin gudanar da bincike a kan matsalar tururuwar
matasa 'yan ci-rani da ke ratsawa ta Jamhuriyar Nijar
daga wasu kasashen Afrika zuwa kasashen Turai.
Hukumomin Jamhuriyar ta Nijar sun ce sun kama shi ne
saboda ba shi da cikakkun takardun izinin gudanar da
aiki.
Sai dai kamfanin jaridar ya ce ma'aikacin nasa ya samu
izinin shiga kasar da gudanar da aikinsa.
Ya kara da cewa ranar Litinin zai ci gaba da tattaunawa
da hukumomin kasar domin a saki dan jaridar.
Title :
An tsare dan jaridar Nigeria a Nijar
Description : Jami'an tsaro a jihar Agadez ta Jamhuriyar Niger na ci gaba da tsare wani dan jarida daga Nigeria da ya je kasar don neman labarai. S...
Rating :
5