Wata likita a Ingila ta bayyana gaban kuliya bisa zargin
aikata kisan wani yaro dan shekaru 6 ba da niyya ba.
Ana zargin Dr Hadiza Bawa-Garba da yin sakaci kuma
abin da ya janyo rasuwar yaron kenan.
Dr Hadiza Bawa-Garba ta shaida wa masu taimaka wa
alkalai yanke hukunci cewa tun tana karama a Nigeria ta
ke son yin aikin likita.
An shaida wa kotun cewar iyayenta ne suka turo ta nan
Ingila karatu kuma ta samu shaidar zama likita a
makarantar koyan aikin likita ta Leicester Warwick.
Ana zargin Dr Hadiza Bawa-Garba da wasu ma'aikatan
jiyya su biyu, Theresa Taylor da Isabel Amaro da aikata
kisa bada niyya ba a asibitin Leicester Royal infirmary a
watan Fabarairun 2011.
Dukkansu ukun sun musanta laifin yin sakaci da aiki
kuma ana ci gaba da sauraron shari'ar.