Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ya ce an samu
ci gaba a harkokin tsaron kasar, wanda shi ne babban
abun da ke gaban gwamnatinsa.
Buhari wanda ya bayyana haka a lokacin da ya karbi
bakuncin babban jami'in tsaro daga Biritaniya, ya ce ba
za a samu ingantacciyar zamantakewa da tattalin arziki
ba idan babu tsaro a cikin kasar.
Rikicin Boko Haram ne babban kalubale da ke gaban
gwamnatin shugaba Buhari musamman a arewacin kasar,
sannan kuma a kudancin kasar akwai kalubale na masu
satar mutane domin kudin fansa.
A jawabinsa a ganawarsa da shugaban kasar a birnin
Abuja, Babban hafsan tsaron Biritaniya, Sir Nicholas
Houghton ya ce ya gamsu kwarai da gaske da irin ci
gaban da Najeriya ta samu wajen yaki da ta'addaci
karkashin shugabancin Muhammadu Buhari.
Janar Houghton ya tabbatarwa shugaban na Najeriya
cewa Biritaniya za ta ci gaba da taimaka wa kokarin da
Buhari ke yi wajen kawo karshen tayar da kayar bayan
kungiyar Boko Haram.
Tun bayan da ya hau kan mulki a karshen watan Mayu,
an kashe mutane fiye da 1,200 a hare-hare masu nasaba
da kungiyar Boko Haram.
Title :
An samu ci gaba a harkar tsaro - Buhari
Description : Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ya ce an samu ci gaba a harkokin tsaron kasar, wanda shi ne babban abun da ke gaban gwamnatinsa. Buha...
Rating :
5