Rahotani sun bayyana cewa an sake samun fargabar
bular cutar ebola a garin Calabar da ke jihar Cross Riba.
Rahotani sun ambato hukumar samar da agaji gaggawa
ta kasar na cewa an kebe wasu mutane goma, bayan
huldar da suka yi da wani mutum da alamonin cutar sun
bayyana a jikinsa.
Sun kuma ce mutumin ya rasu jim kadan bayan da aka
kwantar da shi a asibiti.
A yanzu ana kan gwajin jininsu.
A ranar Laraba hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa
kasashe uku da cutar ebola ta fi yiwa illa- Guinea da
Saliyo da kuma Liberia sun shafe mako guda na farko ba
tare da samun wani da ya kamu da cutar ba tun bayan
bular cutar a shekarar 2014.