Rahotanni daga Jahar Taraban Najeriya na cewa
an sace akalla shanun wasu Fulani guda 150 inda
ake zargin al’umar Jukunawa da yin awon gaba da
shanun.
“Jiya da misalin karfe biyu
na rana, Jukunawa sun zo sun sami shanu na a
jeji, sun zo sun tattaru gaba daya babu yaran
babu shanun, shanun nan za su kai 150.” In ji
Bafulatanin da ya mallaki shanun, wanda kuma
bai bayyana sunansa ba.
Matsalar satan shanu, batu ne da ya kusan zama
ruwan dare a Najeriya inda aka samun aukuwar
lamarin a juhohi irinsu Pilato da Nasarawa da
Benue da ma wasu juhohi da ke arewa maso
yammacin kasar.
“Muna mamakin wannan abu, mun yi kuka ga
gwamnatin Jaha, ba sau daya ba ba sau biyu ba,
shi gwamna mun yi zama da shi a Wukari ya ce a
yi hakuri zai kare dukiyar mu zai kare
rayukanmu, to amma gashi har yau ana kashe mu
a dauke mana dukiya, ban ga kamar gwamnatin ta
na da niyyar kare mu ba.” In ji shugaban
kungiyar Fulani ta Miyetti Allah na Jahar Taraba,
Alhaji Ummaru Mafindi.
To sai dai kungiyar hadin kan Jukunawa a jahar ta
Taraba, ta musanta cewa da saninta ne ake
wannan sace-sacen.
“Zai zama babban kuskure a yi irin wannan zargi,
gaba daya a ce Jukunawa, har yanzu kungiyar
hadin kan Jukunawa na kan bakar ta na cewa a yi
zaman lafiya tsakanin kabilu da ke zaune, babu
ruwanmu da wanda zai tada mana da hankali, ko
kuwa ya je ya yi sata da sunan Jukunawa.” In ji
shugaban kungiyar hadin kan Jukunawa ta
Najeriya, Mr. Bako Benjamin.
Title :
An Sace Shanu 150 a Jahar Taraba
Description : Rahotanni daga Jahar Taraban Najeriya na cewa an sace akalla shanun wasu Fulani guda 150 inda ake zargin al’umar Jukunawa da yin awon gaba...
Rating :
5