Wasu 'yan kunar bakin wake sun ta da bom a Maiduguri
a daren Talata.
Kakakin rundunar soja kasa ta Najeriya Kanar Usman
Kuka Sheka ya tabbatar wa da BBC aukuwar lamarin,
yana mai cewa 'yan kunar bakin wake uku ne suka kai
hare haren a wurare daban-daban a unguwar Ajilari ta
hanyar ta da bama-baman da ke jikinsu kimanin mintina
uku tsakanin juna.
Ya kara da cewa mutane 7 ne suka mutu, cikin su har da
maharan, sannan mutane 11 suka jikkata.
Wannan harin ya zo ne a lokacin da rundunar sojin
Najeriya ke ikirarin samun nasara a kan Boko Haram.