Gwamnatin kasar Nijer ta kafa dokar ta bace na tsahon kwanaki 15 a jihar Diffa dake kudu maso gabashin kasar A wata sanarwa a gidan talbijin din kasar ya fitar a jiya Laraba, gwamnatin ta dauki wannan matakin ne biyo bayan wani hari da kungiyar boko haram ta kai a karshen makun da ya gabata, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 40.
Gwamnati ta ce wannan mataki , shi zai baiwa jami'an tsaro damar karfafa matakan tsaro a yankin.
Dokar ta bacen za ta tsakaita zirga-zirgar shige da fice da kuma shigar kayayyaki cikin jihar ta Diffa, daga watan favrayu zuwa yanzu alkaluma sun ce jihar ta Diffa ta fuskanci hare-haren kungiyar boko haram har so 57, lamarin da ya yi sanadiyar raba mutane kimanin dubu 150 da mahalinsu, a nata bangare gwamnatin Nijer ta tsare kimanin mutane dubu daya da dari guda kan zarkin su da alaka da kungiyar ta boko haram
Title :
An Kafa Dokar Ta Bace A Jihar Diffa Dake Kudu Maso Gabashin Kasar Nijer
Description : Gwamnatin kasar Nijer ta kafa dokar ta bace na tsahon kwanaki 15 a jihar Diffa dake kudu maso gabashin kasar A wata sanarwa a gidan talbijin...
Rating :
5