Kasar Jamhuriyar Benin ta soma zaman makoki na
mako daya don juyayin rasuwar tsoho shugaban
kasar Mathew Kerekou da ya rasu jiya Laraba.
Ba’a dai bada wani
cikakken bayanin abinda ya janyo ajalin
nashi ba, amma tarihinsa ya nuna cewa ya
samu horaswar aikin soja ne a birnin Paris
na Faransa wanda bayansa ne ya koma kasar
tasu wacce a wancan lokacin ake kiranta da
suna “Dahomey.”
A cikin shekarar 1972 ne Kerekou ya kwace
ragamar mulkin kasar ta hanyar juyin mulki
inda ya aiwatarda ita a matsayin kasar dake
bin akidar Kwaminisanci, sannan ya chanja
mata suna zuwa “Benin.”
Bayanda akidar kwaminisancin taki ci ne,
Kerekou yayi watsi da ita, kuma ya maida
kasar a bisa akidar demokradiya inda Benin
ta zama daya daga cikin kasashen Afrika na
farko da suka gudanarda zaben shugaban
kasa na siyasa tsagaronta.
An kada shi a zaben da aka yi na 1991 amma
ya sake samun nasara a 1996 inda kuma yaci
gaba da zama kan karagar mulki har
lokacinda sauye-sauyen da aka yi wa kundin
tsarin mulkin kasar ya tilasta mishi sauka
daga mulki a shekarar 2006.
Title :
An Fara Zaman Makoki A
Jamhuriyar Benin
Description : Kasar Jamhuriyar Benin ta soma zaman makoki na mako daya don juyayin rasuwar tsoho shugaban kasar Mathew Kerekou da ya rasu jiya Laraba. ...
Rating :
5