Majalisar dattawan Nigeria ta dage tantance mutanen da
Shugaba Muhammadu Buhari ya nada su a matsayin
ministoci zuwa ranar Talata.
Majalisar ta bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a
shafinta na Twitter.
Ba ta fadi dalilin dage tantance ministocin ba.
Gabanin dage zaman tantance ministocin na yau, 'yan
majalisar sun amince da ministoci 18 da suka tantance
ranar Laraba.
Kazalika, 'yan majalisar sun jinkirta tantance tsohon
gwamnan jihar Ribas, Rotimi Ameachi zuwa ranar
Alhamis.
Matakin ya biyo bayan rashin mika rahoton kwamitin da'a
da korafe-korafen jama'a na majalisar dattawan da ke
binciken wani korafi a kan Mr Amaechi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar
sunayen mutane 37 ne domin ya nada su a matsayin
ministoci ko da ya ke daga bisani ya janye sunan Alhaji
Ahmed Ibeto daga jihar Niger.
Ana ganin an janye sunan sa ne saboda an aike da
sunayen mutane biyu daga jihar zuwa majalaisar ta
dattawa.