Kotun kula da da'ar ma'aikata ta Najeriya, ta dage
shari'ar da take yi wa shugaban Majalisar dattawan kasar
Bukola Saraki kan zargin yin karya wajen bayyana
kadarorinsa.
Kotun ta ce ta dage shari'ar ne saboda Saraki ya kai kara
zuwa Kotun daukaka kara inda yake son sanin ko kotun
da'ar ma'aikatan tana da hurumin sauraren kara a kansa.
Sai dai kotun ta amince da bukatar lauyoyin masu shigar
da kara cewa a koma gaban ta ranar biyar da shida ga
watan Nuwamba domin ci gaba da sauraren karar, ganin
cewa kafin lokacin kotun daukaka karar ta yanke hukunci
kan bukatar Saraki.
Saraki ya gurfana a gaban kotun ne bisa zarge-zarge
goma sha uku -- cikin su har da zargin yin karya wajen
bayyana kadarorin da ya mallaka.
Ya musanta zarge-zargen a lokacin da ya fara gurfana a
gaban kotun ranar 22 ga watan Satumba.
'Yan Majalisa sun yi masa rakiya
Saraki ya isa kotun da ke Abuja ne tare da rakiyar 'yan
majalisar dattawan kasar su fiye da tamanin.
A cikin 'yan majalisar dattawan har da: mataimakin
shugaban majalisar, Sanata Ike Ekweremadu da
shugaban masu rinjaye, Sanata Ali Ndume da Sanata
Aliyu Magatakarda Wamakko da Sanata Dino Melaye da
Sanata Danjuma Goje.