Majalisar dattawan Nigeria ta tantance sannan kuma ta
amince da mutane 18 domin shugaba Muhammadu
Buhari ya nada su a matsayin ministoci.
Shugaban majalisar, Sanata Abubakar Bukola Saraki shi
ne ya jagoranci zaman wanda aka amince da ministocin
daya bayan daya.
Tun a ranar Talata majalisar dattawan ta tantance
mutane 10 sannan kuma a ranar Laraba ta tantance
mutane 8 inda jumlar ta zama mutane 18.
Majalisar dattawa ta jinkirta tantance tsohon gwamnan
jihar Ribas, Rotimi Ameachi sai zuwa ranar Alhamis.
Matakin ya biyo bayan rashin mika rahoton kwamitin da'a
da korafe-korafen jama'a na majalisar dattawan da ke
binciken wani korafi a kan Mr Amaechi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar
sunayen mutane 37 ne domin ya nada su a matsayin
ministoci kafin daga bisani ya janye sunan Alhaji Ahmed
Ibeto daga jihar Niger.
Ga jerin wadanda aka amince da su:
1. Sanata Udoma Udo Udoma daga jihar Akwa Ibom
2. Kayode Fayemi daga jihar Ekiti
3. Audu Ogbeh daga jihar Benue
4. Ogbonayya Onu daga jihar Abia
5. Osagie Ohanire daga jihar Edo
6. Laftar Janar AbdulRahman Dambazau daga jihar Kano
7. Alhaji Lai Muhammed daga jihar Kwara
8. Hajiya Amina Mohammed daga jihar Gombe
9. Injiniya Sulaiman Adamu daga jihar Jigawa
10. Alhaji Ibrahim Usman Jibrin daga jihar Nasarawa
11. Babatunde Raji Fashola daga jihar Lagos
12. Ibe Kachukwu daga jihar Delta
13. Alhaji Abubakar Malami daga jihar Kebbi
14. Hajiya Aisha Alhassan daga jihar Taraba
15. Solomon Dalong daga jihar Filato
16. Chris Ngige daga jihar Anambra
17. Hadi Sirika daga jihar Katsina
18. Kemi Adeosun daga jihar Ogun
Title :
An amince da ministocin Nigeria 18
Description : Majalisar dattawan Nigeria ta tantance sannan kuma ta amince da mutane 18 domin shugaba Muhammadu Buhari ya nada su a matsayin ministoci. ...
Rating :
5