Shugaban Amurka, Barack Obama ya ce zai ura dakarun
soji 300 zuwa kasar Kamaru domin yaki da Boko Haram.
Sanarwa daga fadar White House ta ce, Obama ya
bayyana aniyyarsa ga majalisar dokokin kasar cewa zai
tura dakarun 300, a yunkurin kawo karshen kungiyar
Boko Haram.
Wani jami'in gwamantin Amurka da ya bukaci a boye
sunansa, ya tabbatarwa da BBC cewa wasu kwamandojin
rundunar sojin Amurkar har sun isa Kamaru.
Ya kara da cewa, dakarun za su dukufa da aikin tattaro
bayanan sirri da cikakkun bincike a kan yadda ake
gudanar da aiki kawo karshen hare-haren Boko Haram.
Kungiyar Boko Haram ta addabi kasashen Kamaru da
Chadi da Nijar da kuma Najeriya inda ta hallaka mutane
fiye da 15,000 a cikin shekaru shida.
Kasashen tafkin Chadi dama suna neman taimakon
manyan kasashen duniya domin kawar da kungiyar Boko
Haram.
Tuni kungiyar Boko Haram ta yi mubaya'a ga kungiyar IS
mai ikirarin kafa daular musulunci.