Shugaban dakarun Amurka na Afrika Janar David
Rodriguez ya bai wa jamhuriyar Kamaru motocin yaki
domin tallafa mata wajen yaki da kungiyar Boko Haram.
Babban jami'i mai kula da kayayyakin yaki na Kamaru
Kanal Jean Jacques Fouda, ya ce motocin za su taimaka
kwarai kuma kasar bata taba samun tallafin irinsu ba.
Duk da cewa Kanal Fouda bai fadi adadin motocin ba,
rahotanni na cewa guda shida kuma an taba amfani da
su a kasar Afghanistan.
A farkon makon nan ne gwamnatin fadar Amurka ta
sanar da tura dakaru 90 zuwa Kamaru, wadda ke daya
daga cikin kasashen da kungiyar Boko Haram ke kai hare-
harenta.
Title :
Amurka ta bai wa Kamaru motocin yaki
Description : Shugaban dakarun Amurka na Afrika Janar David Rodriguez ya bai wa jamhuriyar Kamaru motocin yaki domin tallafa mata wajen yaki da kungiyar...
Rating :
5