Shugabannin sojojin Rasha da Amurka za su gudanar da wani taron gaggawa a tsakanin su dan kaucewa rarrabuwar kawunan da aka samu dangane da hare haren da Rasha ta kaddamar a Syria.
Amurka da kawayenta na ci gaba da nuna shakku kan manufar Rasha na kai hare haren, inda suke zargin cewar Rasha ta kaddamar da hare hare kan ‘Yan Tawayen kasar dake neman kifar da gwamnatin shugaba Bashar al’ Assad, a maimakon kungiyar ISIS.
To sai dai Kasar Rasha ta musanta wannan zargin kuma ta bukaci Amurka ta gabatar da shaida kan cewa ba kan kungiyar ISIS ta ke kaddamar da hare harenta ba.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov sun bayyana shirin gudanar da taron sojin bayan ganawar da suka yi.
Title :
Amurka da Rasha za su gana kan hare haren Syria
Description : Shugabannin sojojin Rasha da Amurka za su gudanar da wani taron gaggawa a tsakanin su dan kaucewa rarrabuwar kawunan da aka samu dangane da ...
Rating :
5