TAMBAYA TA 1747
********************
Assalamu Alaikum.
Malam Dafatar kana lafiya. Malam Ina da tambayoyi Guda 3.
1. Malam Muna Rubuta Jarabawar Karshe na kammala, Karatun mu ina neman addu'oi, akan Allah ya sa mu kammala lafiya.
2. Akwai Wani abokina kuma da ya dade yana neman aiki, amma har yanzu bai daceba, ya na neman addu'oin da zai rika yi, doman ya samu dacewa a aikin da yake nema.
3. Haka akwai wani dan uwana, da ya kasance yayi aikata (Istimna'i) a baya, amma ya daina tsawwon shekara daya kenan, sakamakon fadakarwa da kake kan haramci, da kuma illolin da aikata hakan ke haifarwa, amma yanzu yana fama da kankantar gabansa, kamar da karamin yaro sosai, yana neman taimakon magani malam, dan Allah a taimaka.
Daga wani bawan Allah.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Addu'ar neman Samun dacewa a jarrabawar makaranta, da kuma dacewa wajen samun aikin yi, ita ce:
1. Yawaita Salatin Annabi (saww) domin shi Salatin Annabi (saww) hasken rayuwa ne, kuma Mabudin alkhairai ne. Kuma hanyar yayewar bakin ciki ne.
2. Yawaita ambaton sunan Allah "YA RABBI!!". Domin Malamai da yawa suna ganin cewa shine SUNAN ALLAH MAFI GIRMA. Tunda dashi ne Annabawansa suke kiransa akan bukatunsu.
Maganin da zai sha kuma domin kyautata lafiyar jikinsa, Ya yawaita shan Man Jirjeer wanda aka gaurayashi da man habbatus sauda. Kuma yana shafawa.
In sha Allahu za'a samu biyan bukata.
WALLAHU A'ALAM.