An tabbatar da mutuwar alhazan Najeriya 199 a
turmutsitsin ranar 24 ga watan Satumba a Mina
kasar Saudiya.
Alkaluman da aka bayar
yanzu sun nuna karin mutuwar alhazai 54 bisa ga
adadin da aka bayyana tun can farko.
Kwamishanan labarun hukumar alhazan Najeriya
Shaikh Sale Okenwa ya sanarda hakan a wani
karin bayanai da ya bayar.
Har yanzu ana neman alhazan Najeriya 111 da
kawo yanzu ba'a san inda suke ba ko suna da rai
ko kuma sun rasu. Akwai mutane biyar da ake
jinyarsu.
An yi taron addu'ar bankwana ga alhazan da suka
fito daga kasashen Afirka inda jihar Kebi ta samu
ta ciyar da wasu alhazan. Kanar Samaila Yombe
Dabai mataimakin gwamnan jihar Kebbi ya yiwa
alhazan da suka rasu addu'a.
Sarkin Argungu ya yi korafi kan wurin da ake
ajiye alhazan Najeriya wanda yake da tazarar
kilomita biyar daga wurin jifar Shaidan. Yace an
yi kusan shekaru 20 ana ajiye 'yan Najeriya a
wurin. Ya kamata a canza masu. Sun kuma mika
korafin ga mahukuntar kasar ta Saudiya.