Daga cikin abubuwan ban mamaki wadanda zasu fari aranar Alqiyamah shine: Shine kashe mutuwa da Za'a yi.
Sayyiduna Anas bn Malik (ra) da Abu Hurairah (ra) duk sun ruwaito daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"ZA'A ZO DA MUTUWA ATSAYAR DA ITA AKAN SIRA'DI ARANAR TASHIN ALQIYAMAH. SANNAN SAI AYI KIRA "YA KU 'YAN ALJANNAH!!".
ZASU 'DAGA KANSU SUNA CIKIN TSORON KAR AFITAR DASU DAGA WAJEN DA SUKE... ZA'A TAMBAYESU "SHIN KO KUN SAN WANNAN?"
ZASU CE "EH MUN SANTA. MUTUWA CE YA UBANGIJI"
SANNAN ZA'A KIRA 'YAN WUTA "YA KU 'YAN WUTA!!". ZASU 'DAGA KAI CIKIN MURNA. SUNA ZATON KO ZA'A FITAR DASU NE DAGA AZABAR DA SUKE CIKI.
SAI A TAMBAYESU "SHIN KUN SAN WANNAN?"..ZASU CE "EH MUN SANTA MUTUWA CE".
ZA'A SAKE BADA UMURNI,SAI A YANKATA AKAN SIRA'DI. SANNAN ACE MA KOWANNE DAGA CIKINSU "ZAKU RAYU AWAJEN DA KUKE NE HAR ABADA. BABU MUTUWA".
(Imamu Ahmad ne ya ruwaito hadisin).
************************
Daga wannan ranar 'Yan wuta zasu shiga bakin cikin da ba zai yanke agarezu ba, har abada. Su kuma 'Yan Aljannah zasu yi farin cikin da ba zai yanke ba.
Ya Allah ka tsunduma dukkan daliban ZAUREN FIQHU acikin aljannah tare da dukkan iyayensu da iyalansu da masoyansu da malumansu da dukkan Musilmai baki daya.
Ya Allah ka nisantar damu daga wuta, da dukkan ayyuka da zantukan da suke kusantarwa zuwa ga wutar!!!
Aaameeen
DAGA ZAUREN FIQHU FACEBOOK.