Ma'aikatan kotunan jihar Taraba sun shiga yajin
aiki saboda suna neman gwamnati ta bar kotunan
jihar su dinga cin gashin kansu kamar yadda
dokar kasa ta amince.
Yajin aikin da ma'aikatan
suka shiga yi ya jefa lauyoyi cikin wani halin
rudani da kuma wadanda suke jiran hukunci.
Ma'aikatan sun shiga yajin aikin ne saboda
fafutikar da suke yi na neman a baiwa fannin
shari'a daman cin gashin kai ta hanyar basu
kudade kai tsaye kamar yadda wasu jihohi suka yi.
Ita ma gwamnatin tarayya ta yi hakan.
Rashin aiwatar da shirin cin gashin kansu ya sa
ma'aikatan kotunan suka shafe fiye da watanni
shida suna yajin aiki. Lamarin ya haifar da
cunkoso a ofisoshin 'yansanda tare da kawo jinkiri
wajen yanke shari'a.
Muhammad Usman Karim shugaban kungiyar
ma'aikatan kotuna ya bayyana dalilinsu na
komawa yajin aiki. Yace gwamnati ta nuna masu
halin ko inkula bisa ga yarjejeniyar da suka yi shi
ya sa suka koma yajin aikin.
Lauyoyi sun nuna bacin ransu game da wannan
dambarwar dake tsakanin ma'aikatan da
gwamnatin jihar. Barrister Idris Abdullahi Jalo
shugaban kungiyar lauyoyin jihar yace yajin aikin
ya jefasu cikin halin tsaka mai wuya. Yace yajin
aikin koma baya ne wajen cigaban aiwatar da
shari'a.
Title :
A Jihar Taraba Ma'aikatan Kotuna
Sun Shiga Yajin Aiki
Description : Ma'aikatan kotunan jihar Taraba sun shiga yajin aiki saboda suna neman gwamnati ta bar kotunan jihar su dinga cin gashin kansu kamar y...
Rating :
5