.. Adadin mutanen da suka rasu a turmutsutsun da aka yi
lokacin aikin hajjin bana a Saudiyya ana tsammanin
yanzu ya kai akalla mutane dubu daya da dari shida da
ashirin.
An dai samu wannan adadin ne daga jami'an harkokin
wajen kasashen da suke da mutanen da suka je aikin
hajjin na bana.
Wannan dai ya kasance hadari mafi muni da aka taba
samu a lokacin aikin hajji a tarihi.
Adadin da ma'aikatar lafiya ta Saudiyyan tabayar dai dari
bakwai da sittin da tara ne.
'Yan Nigeria 168 ne hukumomin kasar suka ce sun rasu
sakamakon hadarin na ranar Idi.
Title :
'Alhazai 1,620 ne suka rasu a Saudiyya
Description : .. Adadin mutanen da suka rasu a turmutsutsun da aka yi lokacin aikin hajjin bana a Saudiyya ana tsammanin yanzu ya kai akalla mutane dubu...
Rating :
5