Shugaban Najeriya Muhammadu Buahari ya bayyana
cewa nan ba da jimawa ba, za a gurfanar da wadanda
suka yi almubazzaranci da biliyoyin kuadade mallakan
Kamfanin mai na Kasar, NNPC.
Buhari ya fadi haka ne a ganawar da ya yi da shugaabn
Kasar China Xi Jinping a jiya lahadi a birnin New York na
kasar Amurka.
Buhari ya kara da cewa gwamantinsa a shirye take domin
tabbatar da tsafta a Kamfanin NNPC ta yadda zai kubuta
daga matsalar cin hanci da rashawa.
To sai dai shugaban na Najeriya bai sanar da lokacin da
za a gurfanar da wadanda ake zarigi da almubazzaranci
da kudaden ba.