TAMBAYA TA 1708
********************
Assalamu alaikum Malam. Allah ya saka maka da alkhairi bisa taimakon da kake yi mana.
Don Allah Malam ina neman shawara ne ko addu'ar da zan rinka yi. Ina cikin matsala ne akan lamarin Maigidana. Ba ya ganin mutuncina balle mutuncin iyayena.
Duk wani zagi na cin mutunci yana min Kuma ko agaban yarana. har ya kai min hanu. iyayena inzai fadi magana akansu ba girmamawa agabana, baya son min abu koda hakkina ne amma zaiyi wa wasu.
Mal yana da kyashi, gaba, Kullum mukayi fada ko shine bayida gaskiya zan mai sallama d gaisuwa bazai amsa ba se Randa yaga dama yanzu munkai wata guda baya yimun magana don kawai ina girki kero yakare na gaya mai km kfin nanma nagaya mishi to abin bukata in babu bazai sayaba har tafiya yayi ya barmu ba abinci 4 10dys Mal kuma harga Allah nagaji da kaiwa Kara tunda ba denawa yakeba sede yakara sabon salo Kuma KO an gaya mai gsky baya dauka sbd girman Kai baya sauraran damuwana da bukatuna bai damu da yaransa ba.. ko yaro zai mutu yana kuka in Ina wani Abu ko bayida lfy bazai dagashi ba.Mal takaicin danakesha bazai kirguba atsawon 8yrs kuma Ina addu'a banana wasaba. nagode
(Daga wata Baiwar Allah)
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Shi aure ana yinsa ne domin cika Umurnin Allah da kuma koyi da sunnar Manzonsa (saww).
Don haka komai yayi zafi idan akayi hajuri zai wuce. Kar kiyi gaggawar yanke hukuncin fita daga hannun Mijinki. Duk munin halinsa kici gaba da hakuri dashi. Ko don mutuncin wadannan yaran da kuka haifa, da kuma kyautatuwar tarbiyyarsu.
Ki duba ki gani: Shin haka auren naku yake tun daga farko? ko kuwa daga baya ne wannan rashin jituwar ta shigo muku?;«
Idan sai daga bayan nan ne kuka fara samun rashin jituwa, to sai ki duba kiga shine menene ya kawo hakan? idan a naki bangaren ne sai ki gyara domin asamu zaman lafiya.
Idan kuma daga bangarensa ne sai kiyi kokarin nusar dashi kuskurensa cikin nasiha da lallami. Na tabbata in dai mai cikakken hankali ne zai yarda ku zauna tare ku sulhunta tsakaninku.
Duk wanda kika ga yana zaman aure, to kodai yana hakuri ne da abokin zamansa, ko kuma shi din ana yin hakuri dashi. Kuma kasancewar Mijinki shine kofar shiga Aljannarki, to Allah zai iya jarrabaki ta hanyar hadaki da kangararren mutum.
Kiyi hakuri ki dubi rayuwar 'Ya'yanki. Idan har kika fita daga gidan mahaifinsu to rayuwarsu ba zata ta'ba komawa daidai ba. Kuma kema duk inda kikaje zakiji hankalinki yana kan 'Ya'yanki. Don haka gara kiyi hakuri ki zauna ki rikesu. Watakil acikinsu zaki samu wanda zai rika huce miki zuciya daga halin da kike ciki.
Shi kuma abangaren Mijinki, indai da gaske ne yana zagin iyayenki, to watakil dama ba ya ganin mutuncin nasa iyayen ne. Babu mutumin da zai raina surukansa har ya rika zaginsu sai wulakantacce.
Da wannan nake cewa ki dage da addu'a. Musamman "YA HAYYU YA QAYYOUM BIRAHMATIKA ASTAGHEETHU, FA ASLIH-LEE SHA'ANEE KULLAHU WALA TAKILNEE ILA NAFSEE TARFATA 'AININ".
"يا حي ياقيوم برحمتك أستغيث فأصلحلي شأني كله ولا تكلنى إلى نفسي طرفة عين "
Ki yawaita wannan addu'ar Allah zai taimakeki ya kawo miki yayewar wannan damuwar. Kuma Allah zai tsaya miki acikin lamarinki gaba daya.
WALLAHU A'ALAM.
ZAUREN FIQHU