TAMBAYA TA 1709
*********************
Assalamu alaikum warahmatullah. Malam don Allah a taimaka min tunda nayi rashin lafiya na rame amma yanzu na warke, na dade da warkewa don nafi shekara amma har yanzu ban maida jikina ba. Yawancin abubuwa masu gina jiki ina ci, nasha multivitamins amma abin yaci tura. Shine nakeso a taimaka min ko Allah zaisa a dace. Bissalam.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Ai ita Qiba ayawancin lokuta ba abin so bane. Don min kuwa tana janyo ma masu ita su rika jin nauyin jiki da kuma yawan jinya fiye da Siraran mutane.
Amma idan kana sin mayar da jikinka ne, to ka yawaita amfani da hulba. Ka rika dafa cokali guda nata, kana sha kullum da safe tare da Zuma ko Sugar. In sha Allahu zaka samu jikinka ya dawo cikin kankanin lokaci.
Ka yawaita amfani da ita kanta zuma din. Zata gyara maka Kayan cikinka. Musamman Tumbinka da hantarka da hanjin cikinka. Don haka cikinka zai bude yadda zaka ci abinci sosai. Sai jikinka ya Girma cikin kankanin lokaci.
ALLAH ya sawwake.
WALLAHU A'ALAM.
Source ZAUREN FIQHU WHATSAPP