Malam ya hidima damu.ALLAH ya jikan magabata da rahama, mu kuma yasa mu cika da imani. ALLAH ya hadamu a aljanna firdausi.
Malam ina matsalane akan maganin da ka rubuta na cuta mai karya garkuwar jiki. matsalar itace ruwan zam zam nada wahalar samu awajen da nake ahalin yanzu. naje ance min sunyi wahalar samu ne. Kuma gashi ba kusa nake da kano ba. shine nake son ataimaka asama min wata hanya ta magance wannan matsala.
Sai abu na biyu tambayace. Yaya anfanin ruwan zogale da icce darbejiya yake ga mai wannan cuta?.
na uku kuma shin maganin da ake bayarwa a asibiti miye tasirin hadashi da wannan na islama awajen warkar da cutar? kuma za'a iya anfani da biyu din lokaci guda?
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.
1. In dai anan Nigeria kake, babu wata jiha wacce ba zaka samu ruwan zamzam ba. in dai akwai Musulmai acikinta. idan ma babu musulmai awajen, ai zaka ita bayar da sautu asayo maka ruwan zamzan din daga Kano ko Kaduna, ko kuma wani babban birni anan arewacin Nigeria.
Ni dai ban san wani ruwan da zan gaya maka maimakon ruwan zamzam ba. Shine MAFIFICIN RUWA wanda Allah ya bulbulo dashi agarin Annabi Muhammadu domin shayar da Kakan Annabi Muhammadu (saww).
Kuma Annabi (saww) ya fadi fa'idodinsa da dama. Yace shi waraka ne daga chututtuka. Kuma yace shi yana aiki ne akan duk abinda aka shashi dominsa.
2. Gaskiya ban san tasirin da itacen darbejiya yake dashi game da chutar Aids ko HIV ba. Ni dai na san cewa itacen yana kunshe da sinadaran magunguna da dama.
3. Mu dai a Likitancin Musulunci ba ko yaushe muke hana marar lafiya yin amfani da magungunan asibiti ba. Kuma na san mutane da dama wadanda suka dena amfani da magungunan asibiti, sun dogara da magungunan Musulunci. Kuma da haka suka samu sauki daga wannan chutar.
Ka dogara ga Allah ka kiyaye shawarwarin da muka baka tun farko. Dukkan waraka ahannun Allah take, kuma yana bayarwa ga wanda yaso, alokacin da yaso.
WALLAHU A'ALAM.