Assalamu alaikum.
Allah Ya kara wa Malam Iymani, fahimta, lafiya da kwanciyar hankali.
Ina tambaya ne game da kallon wasan kwaikwayo na hausa da na yare a dvd ko a satlait da iyaye da abokanmu da mu muka cika gidajen mu da Tibunan kallo wanda ya mayar da mai da hankali wajen bitan darussan makaranta kauyanci.
Kuma menene hukuncin sayar da faifen VCD na wasan hausa?
Tambaya daga Almajirin ka me kaunar ka Alfanu Rishi.
Abdu Bello Rishi 9/7 sarki street yankolli jos
Nigeria
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Hakika Ubangijin da ya haliccemu yayimu ne ba don wasa ba. ya haliccemu ne ya sanya mana numfashi ya rayamu aduniya domin muyi kyakkyawan amfani da wannan lokutan wajen neman yardarsa ta hanyar shagaltuwa da bautarsa.
Kallon wasan kwaikwayo ba laifi bane idan ya zamto babu kida acikinsa, babu rawa, ko wakokin soyayya, babu nuna tsaraici, kuma babu taba jikin juna tsakanin maza da mata, kuma bai kunshi abubuwan da suka sa'ba ma shari'ah ba.
Amma idan ya zamto ya kunshi harantattun abubuwa kamar su ki'da da wakokinsu na shashanci, ko rawa tsakanin maza da mata, ko kuma bayyana tsaraici, ko taba jikin juna, Ko kuma sauran abubuwan da zasu iya karkatar da zukatan al'ummah, to Haramun ne kallon wasan kwaikwayon, kuma haramun ne sayar dashi ko dillancinsa. Kuma su ma masu yinsa wajibi ne su tuba zuwa ga Allah.
Wadannan lalatattun abubuwan sun taka rawa wajen lalata tarbiyyar yaran Musulmai da kuma dauke hankulansu daga kan karatun Alqur'ani da zikirin Allah da sauran abubuwa masu amfani.
Da fatan al'ummah zasu yarda su gyara wadannan abubuwa tun daga gidajenmu.
WALLAHU A'ALAM.