Manzon Allah (saww) ya kasance idan zai yi harama yakan sanya turare mafi dadin Qamshi wanda ya samu gareshi.
(Imamu Muslim ne ya ruwaito)
- Ya kasance idan "YAUMUT TARWIYYAH" ta zama saura kwana daya yakan yiwa mutane Khutubah, ya sanar dasu yadda zasu gudanar da aikin hajjinsu.
(Hakim da Baihaqiy ne suka ruwaitoshi).
Ya kasance idan yana TAWAFI a dakin Ka'abah yakan sumbanci Hajrul Aswad da kuma Ruknul Yamaniy akowanne Tawafi".
(Ahmad da Hakim ne suka ruwaitoshi)
Ya kasance Ba y'all substrate komai in banda Hajrul Aswad da ruknul yamaniy".
(Jami'us Sagheer)
Ya kasance idan har ya jefi Jamratul Aqabah ba ya tsayawa, Wucewa yake yi".
(Sahihul Bukhariy)
"Ya kasance yana yin raka'a biyu (Qasaru) a Mina".
(Bukhariy da Muslim ne suka ruwaitoshi".
"Ya kasance idan yana dawowa daga wajen Yaqi, ko aikin Hajji ko Umrah, yana yin kabbara sau uku idan yazo kowanne Tudu. Sannan yace: "LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU. LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, WA HUWA 'ALA KULLI SHAY'IN QADEER.
AAYIBUBA, TA'IBUNA AABIDUNA, SAJIDUNA, LIRABBINA HAMIDUN.
ALLAH YA CIKA ALKAWARINSA, KUMA YA TAIMAKI BAWANSA. KUMA YA TARWATSA RUNDUNONIN (KAFIRAI) SHI KADAI".
(Bukhariy da Muslim ne suka ruwaitoshi).
Ya Allah ka Qara son Manzon Allah (saww) ka Qara mana riko da sunnoninsa.
source ZAUREN FIQHU WHATSAPP