Girgizar kasa mai karfin awo 6.6 ta afku a Indonesiya inda mutane 60 suka sami raunuka.
Hukumar bincike game da girgizar kasa ta Amirka ta bayyana cewa, girgizar ta afku da misalin karfe 1 na dare a yammacin yankin Papua, kuma a karkashin teku da nisan kilomita 64.
Kusan gidaje 200ne girgizar ta lalata.
Kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta Indonesiya Sutopo Purwo Nugroho ya fitar da sanarwa cewa, girgizar ta dauki tsawon mintuna 2 tana kadawa.
Mahukunta sun ce, babu barazanar afkuwar Tsunami a yankin.
A shekarar 2004 mutane dubu 230,000 ne suka mutu sakamakon afkuwar girgizar kasa kasar ta Indonesiya.