Ba sai kayi amfani da wasu abubuwaba, kawai ka tabbata kana da USB CABLE na android din.
Kaje kan SETTINGS na wayarka xakaga DEVELOPER OPTIONS sai kashiga anan xakaga USB DUBUGGING sai kawai kayi TICK akansa.
Daga nan sai kayi connect din wayar da laptop din ta hanyar USB CABLE din. Idan suka hadu sai kaje SETTINGS na wayarka xakaga MORE idan kashiga xakaga TETHERING & PORTABLE HOTSPOP to idan kashiga xakaga USB TETHERING sai nan ma kayi TICK akai kawai.
Idan kayi haka to kaduba daga kasan pc din xakaga alamar network dinka yana searching. Idan yagama xakaga yatsaya sai kawai kafara browsing takan system din naka.
Amma dole fa sai ka kunna ainihin DATA din Android din.
Ina fata wannan dan bayanin ya gamsar dakai? Harma da wanda baisaniba.
Kabi abin a hankali dan indai kayi yadda nace to xaiyi connecting.
ABIN LURA: Idan wayarka tana cikin Security to yawanci takanki yin connecting gaskiya dan haka sai ka kula.
Wajen Tick na farko wato na wajen DEVELOPER OPTIONS idan kayi sau daya to shikenan, idan kuma kaganshi already ticked to no need kasakeyi. Na biyun ne dole ne duk sanda xakayi connecting din to sai kaje kayi Tick din, kuma idan baka hada wayar da system dinba to idan kaje wajen xakaga yayi Duhu alamar ba dama ayi tick akansa, amma da xarar kahada wayar da system din to xakaga yanunamaka kuma yabaka damaryin tick din.