Kafin tashin Alkiyamah sai duniya ta dauki ado iri iri. Mazauna cikinta sun Qawatata, sun sakankance kamar ba zasu mutu su barta ba. Suna tsammanin cewa babu ranar da zasu Qare, Basuyi tsammani ba ashe ALQIYAMAH tana gab dasu.
Sayyiduna Ubayyu bn Ka'ab (ra) yace:
"Akwai alamomi guda shida wadanda zasu faru kafin ranar tashin Alkiyamah.
Yayin da mutane suna tsakiyar cin kasuwarsu, za'a tafiyar da hasken rana (zata dusashe).
Suna cikin wannan halin sai duwatsu da dogayen tsaunuka su rugurguje su zubo Qasa. Sai Qasar ta fara girgiza ta tsattsage ta chakude.
Aljanu zasu tafi neman mafaka awajen 'Yan Adam. Su ma 'Yan Adam din zasu tafi neman mafaka awajen Aljanu.
Dabbobin gida da na daji, da tsuntsaye zasu chakudu su rika yin karo da junansu (Babu wajen gudu. Subhanallah).
Aljanu zasu ce ma Mutane "Mun zo muku da labari ne. Sai su tafi zuwa ga Manya manyan Tekuna zasu tarar dasu sun kama da wuta.
Suna cikin haka sai Qasa ta keche (ta tsage kenan) tsagewar da sai takai tun daga Qasan bakwai har zuwa Sama ta bakwai.
Suna cikin wannan halin sai wata iska ta buso garesu, wacce zata sanya su mutu (gaba dayansu).
Ibnu Abid Dunya ne ya ruwaito wannan hadisin.
Anan ZAUREN FIQHU WHATSAPP kwanakin baya mu. Kawo jerin alamomin kusantowar tashin Alkiyamah har guda Arba'in ko hamsin da wani abu.
Ya Allah kasa mu cika da imani. Allah ka kiyaye mana imaninmu. Mu rayu dashi, mu mutu dashi, kuma mu tashi dashi aranar Alqiyamah. Kuma Allah ya tashemu acikin tawagar Annabawa da Siddiqai da Shaheedai da Salihan bayinsa.
Aaameeen.