Na wuce daki na kulle kaina ciki, na dauki waya na kira deen dina,
ringing daya ya dauka, hello my hulwah.! Bansan Lokacin da wasu zafafan
hawaye suka qanqarominva, tabbas saidai akasheni baxan iya rabuwa da
deen ba, bazan iya rayuwa idan bashiba.! Hulwaty kinyi shiru, na kasa
magana sai na kashe wayar ya kira sau uku a na hudu na daga, ina dauka
na rushe masa da sabon kuka hankalinsa idan yayi dubu saida ya tashi na
gaya masa aure za'amin a wannan watan, kukana ya qaru, yayi shiru, chan
yafara magana muryarshi na rawa tana sassarqewa, damaa nasan ba sona
kikeba,!! dama nasan yaudarata kike! Shi yasa kikaqi nunamin hatta
gidanku.. tuntuni kinsan an miki miji miyasa kika koyamin qaunarki?
Miyasa kika bari na shaqu dake? Miyasa kika bari saida nakai haka sannan
zaki gaya min cewa an miki miji?? Kinsan kina da wanda zaki aura miyasa
kika shigo rayuwata?? Kin cuceni hulwa! Zaki azabtar da zuciyar da ta
mutu akanki! Wallahi tallahi bazan juri ganinki tare dawaniba a matsayin
mijinki, idan kuwa har hakan ta kasance ina mai tabbatar miki zan iya
rasa rayuwata! Baibarni nace komai ba ya kashe wayar, nayi kira har na
gaji yaqi dagawa qarshe ya kashe wayar! Tabbas zan shiga tsaka mai wuya,
wallahi bazan iya barinkaba deen koda zan rasa rayuwata, kaine farin
cikina! Kaine rayuwata! Kaine ganina! Wani sabon kuka yaci qarfinta,
"tabbas abdool yayi gaskiya da yace so ya mayar da shi makaho mahaukaci
kurma wawa, mara bin umurni mara ra'ayin kanshi'" sai yanzu nake
fahimtar abinda yake cewa! Namiqe a fusace na nufi qofa bana gani Sosai
jiri jiri nake gani dama gani ba auki ba, amma haka na nufi dakin inna,
da nakai bakin qofa kuma sai nayi turus, tabbas bazan iya bijirewa
mahaifiyataba koda zan rasa raina, kuma bazan iya haqurin rashin deen
dina ba! To ina mafita??? Babu...!!
Ba abinda nake tunani illah ranarda za'a daura min auri da wani ba deen dina ba!
Haka na juyo jiki ba qwari na dawo daki naci gaba da kuka, gashi kiran duniya nayiwa wayar deen dina amma a kashe,!
Da wanne yakeson inji? Da baqin cikin auren wanda baya sona koda baqin cikin rabuwa dashi??
Haka nayi sati daya a daki banachin komai sai tea, kuma inna ko ta
kaina batayiba, ga deen dina wayar shi a kulle, yau da safee ina zaune
na hada kai da guiwa, kawai naji qarar wayata banyi niyyar dagawaba da
naga baquwar number sai kuma na daure na daga, abokin deen yake shaida
min deen ba lafiya yana asibiti yau kwana shida kenan hankalina ya gama
tashi, na rarrafa naja mota sai asibiti ina shiga na hadu da tsohuwar
qawata sista khadee itada ammar dinta tana mishi iyayi shi kuma yana
biye da ita, tamin kallon mamaki, tanamason tamini magana amma ni banyi
takantaba,dan hankalina baya tare dani kallo daya na mata na kauda kai
Na shiga inda akacemin an kwantarda deen dina..ina zuwa naga ya rame
yayi wani iri, na matsa kusa dashi kamar in fada jikinsa in nuna masa
sonda nake masa da missing dinsa da nayi amma kuma ba hali, haka na
daure nayi tsaye ina kallonsa ina kuka, qamshin turarena ne ya daki
hanchin sa hakan. yasa ya bude idonsa yana ganina ya rufe idonsa ya
juyan baya, Bashir bashir, yanxu ma Wallahi idan na bude ido ita nake
gani, qamshinta nakeji, please ka kawo min hulwaty na..!!! Yanda yake
magana yasa ta fashe da kuka, hakan yasa deen ya bude idonsa a hankali
ya tabbatar da ba gixo take mar ba, sai kuma ya chanxa xance miya kawoki
gurina....??