Rahotannin dake fitowa daga Najeriya na cewa jami’an tsaron farin kaya na SSS sun gano wani daki, cike da takardun kudin Dalar Amurka a gidan gwamnan jihar Akwa Ibom, dake kudancin kasar.
A baya an bayyana cewa an sami makamaim a gidan, to sai dai kuma wata jaridar kasar ta rawaito daya daga cikin jami’an SSS din na cewa basu sami makaman da aka yi zargin akwai a cikin gidan ba, illa kawai wani dakin dake cike da takardun kudin suka samu.
Daga farko jami’an tsaron sun yi tunanin kwashe kudaden zuwa ofishinsu, amma kuma wasu shugabanninsu dake Abuja suka basu umarnin barin kudin.
Rahoton ajiye makamai a gidan gwamnati, da aka kaiwa hukumar ta SSS ne ya sa jami’an suka kai samame a Jihar, don daukar mataki a kai.
Dama har yanzu gwamna mai ci, Udom Emmanuel bai shiga gidan gwamnatin ba, inda wasu ke cewa har yanzu akwai bangaren da tsohon gwamna Godswill Akpabio ke zaune a wani sashensa.
Jami’iyyar adawa ra PDP a Najeriya tayi Allah wadai da samamen da jami’an na SSS suka kai.