Tabbas yazo acikin Hadisai ingantattu cewa Azumin ranar Ashurah yana kankare zunuban shekara guda, shi kuma na ranar Arfah yana kankare zunuban shekaru biyu. Wacce ta wuce da kuma wacce zata zo.
MENENE DALILI KO HIKIMA AKAN HAKA??
Ibn Qayyim Al-Jauziyyah ya bada amsa kamar haka:
1. Hikima ko dalili na farko shine : Shi Watan da ake yin arfah acikinsa, Wata ne mai alfarma kuma atsakiyar watanni masu alfarma guda biyu yake. Wato yana tsakanin Dhul-Qa'adah da Almuharram kenan.
Shi kuwa watan da ake yin azumin ashurah bai samu wannan ba.
* Hikima ta biyu: Saboda shi Azumin Arfah yana daga cikin kebantattun abubuwan da shari'ar addininmu na Musulunci yazo dashi. Shi kuma Ashurah bai samu wannan ba. Don haka aka ninninka ladan Azumin Arfah don albarkacin Annabi Za'babbe (saww).
(aduba cikin Bada'i'ul Fawa'id juzu'i na 4 shafi na 211).
2. MAI YASA AKE KIRAN RANAR ARFAH DA WANNAN SUNAN? (WATO "ARFAH").
Abul Faraj Ibnul Jawzee yana da amsa akan haka. Yace:
"An sanya ma ranar nan wannan sunan ne (wato yaumul arfah - ranar ganewa) saboda Mala'ikah Jibreelu ya kasance yana nuna ma Annabi Ibraheem (as) wuraren rukunan aikin Hajji. Sannan yace masa "KA GANE WANNAN, KA FAHIMCI WANNAN?".
Dalili na biyu kuma saboda awannan wajen, awannan ranar, kuma akan wannan dutsen ne Kakanmu Annabi Aadam (as) ya hadu da matarsa Wato Nana Hauwa'u bayan saukowarsu daga Aljannah.
Aduba Kashful Mishkal juzu'i na 2 shafi na 156).
3. TA YAYA AZUMIN RANAR ARFAH ZAI KANKARE ZUNUBAN SHAEKARAR DA ZATA ZO?
Imamul Manaawiy yana da amsa. Yana cewa:
"Akwai hikimomi ko dalilai guda uku masu yiwuwa.
A. Albarkar azumin zata kiyayeshi daga aikata zunuban.
B.) Ko kuma za'a bashi lada mai yawa wanda zai shafe masa dukkan zunuban da zai gabatar ashekarar da zata zo.
C. Zai kankare zunuban ne a hakika. Koda sun afku. Wato zai zama mai kankarewar ya rugayi abin kankarewar kenan.
(Aduba cikin FAIDHUL QADEER juzu'i na 4, shafi na 230).
4. SHIN WACCE HIKIMA CE TASA AKA FIFITA AZUMIN RANAR ARFAH SAMA DA AZUMIN RANAR ASHURAH??
Al-Hafiz Ibnu Hajr Al-Asqalaniy yana da amsa kamar haka:
Hakika Azumin ranar Arfah yafi falala fiye da azumin ranar Ashurah. Kuma Malamai sunce hikimar anan ita ce saboda shi azumin Ashurah yana da nasabah ne zuwa ga Annabi Musa (as). Shi kuwa Azumin Arfah ana jinginashi ne zuwa ga Annabi Muhammadu (saww). Don haka ne falalarsa tafi yawa".
(aduba Fat'hul Baariy juzu'i na 4 shafi na 249).
5. SHIN AZUMIN RANAR ARFAH YANA KANKARE MANYAN ZUNUBAI NE? KO KUWA QANANAN YAKE KANKAREWA KADAI?
AMSA: Yana kankare Qananan zunubai ne. Amma banda manya. Kamar su Zinah, madigo, Gulma, Shan giya, Sata, da sauransu, DOLE akwai bukatar sai mutum ya tuba, cikakkiyar tuba wacce ta cika sharudanta. Sannan Allah ya yafe masa.
6. MENENE HUKUNCIN MUTUMIN DA YA DAUKI AZUMIN RANAR ARFAH, ALHALI ANA BINSA AZUMIN RAMADHAN??
AMSA: Wannan azuminsa yayi. Kuma ya inganta. Sai dai anfi son ya gaggauta ramukon abinda ake binsa.
7. SHIN ZAN IYA AZUMTAR RANAR ARFAH KO ASHURA KODA SUNZO ARANAR ASABAR??
AMSA: Eh ya halatta ka azumci ranar Arfah ko ashurah koda sunzo aranar asabar ko lahadi, duk daya suke da kowacce rana. Domin wadannan azumin kowanne Sunnah ne mai zaman kansa. Kuma Hadisin da yake maganar haramcin yin azumi ranar asabar DHA'EEFI ne. Bai inganta ba, kuma ya sa'ba ma wasu hadisan wadanda suka fishi inganci.
8. NI DA BANJE HAJJI BA, MENENE HUKUNCIN YIN WANNAN AZUMIN AKAINA:
AMSA: Malamai da dama sun tafi akan cewa yin azumin ranar arfah ga mazaunin gida, SUNNAH ce mai Qarfi.
9. WANDA BAI SAMU DAMAR YIN AZUMIN NAN BA, WACCE HANYA ZAI BI DOMIN SHIMA YA SAMU LADA?
AMSA: Zai iya tanadar kayan shan ruwa (buda baki) da 'yan soye-soye sannan ya gayyaci masu azumin suzo gidansa suci. Ko kuma ya kai musu inda suke. In sha Allah Ubangiji zai bashi lada kwatankwacin nasu, ba tare da an tauye komai acikin nasu ladan ba.
Nan zamu tsaya da fatan Allah shi taimakemu, Allah shi amsa mana dukkan rokonmu ya yafe dukkan zunubanmu ya tallafi dukkan lamarinmu, ya kyautata karshenmu, ya inganta bayanmu, ya sanyamu acikin Tawagar Muhammadur Rasulullahi (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) aranar tsaiwa.
An gabatar da karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP (4) aranar arfah, Larabah 9 ga Dhul Hijjah 1436 da misalin Qarfe daya na rana.