Salam alaikum, Mallam ina mai mika godiyata ga Allah ubangijin talikai. Mallam Allah ya bamu abinda muke nema duniya da lahira baki daya. Allah ya jarabceni da mata, kuma auren ko shekara daya bai cika ba. amma kullum ina cikin damuwa da zulumin rayuwa kamar ba aure nayi ba.
Ina kyautata mata matukar gwargwado amma duka abanza, kullum a binciken wayata take idan taga lambar wata ko yar uwata sai ta kira ta zage ta kamar ba musulma ba.
Kuma bata daukar nasiha domin baxa ta tsaya ta saurareni ba ma ballantana ta fahimta. A dalilin kanwar aminina ta furta tana sona, ta kirata ta zage ta gaba daya har iyayenta tamkar bata taba saninta ba a rayuwa.. daga karshe ta shirya ta tafi gidansu wai sai na auro waccan ta zauna. Hakika na shiga cikin damuwa musamman na kin kyautatawa yan uwana musammam wanda suka zamo babu aure. Ta yanke alaka tsakaninta da matan aminaina. Na fara tunanin ko ayi mata ruqya amma nace bari na nemi shawarwari daga gareka. Mallam a taimaka min domin ina bukatar shawara da wuri domin ta kure ni da ina ganin zan hakura da ita kawai. Na gode bissalam.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Bawan Allah hakika kana cikin Musiba dalilin faruwar wadannan abubuwan. Amma Hakika dole sai ka daure amatsayinka na mumini. Dama Ubangijinmu ya rantse cewa sai ya jarabcemu.
Kuma Manzon Allah (saww) yace : "BABU WATA MUSIBAH WACCE ZATA SAMU MUMINI FACHE SAI AN KANKARE MASA ZUNUBANSA SABODA ITA. KODA QAYA YA TAKA".
(Sahihu Muslim)
Kaga kenan ashe wadannan abubuwan da matarka take yi maka, idan ka daure zai iya zama hanyar samun lada mai yawa agareka.
Su mata an haluccesu ne daga Qashin Hakarkari Lankasasshe. Shi yasa halayensu da dabi'unsu suke a karkace. Idan kace sai ka mikar dasu, to sai dai ka sakesu.
Manzon Allah (saww) yace: "A BAYANA BAN BARMA MAZAJE WATA FITINA WACCE TAFI CHUTAR DASU FIYE DA MATA BA".
(Wato mataye sune mafi girman fitina agaremu. mu mazajensu).
Din haka kayi hakuri duk matar da take da irin wadannan bakake. halayen watakil tana da Jahilci a bangaren ilimin addininta. Don haka nake baka shawarar ka sanyata a Islamiyyar matan aure.
Bayan haka kuma watakil tana da Aljanu ajikinta wadanda suke mamaye zuciyarta da jikinta. Harma su sanya ta rika furta miyagun kalamai ba tare da saninta ba. Har ma ta rika jin haushinka Kai mijinta, tana munana maka. Don haka ka garzaya da ita cibiyar Magungunan Musulunci mafi kusa daku domin samun agajin gaggawa.
Duk wadannan abubuwan sukan faru sosai acikin Al'ummah. amma babban magani dai shine Hakuri da kuma addu'ar neman shiriya.
ALLAH YA SAWWAKE.
WALLAHU A'ALAM.