Akwai wani lokacin da wasu shaitanun Aljanu suka fitini wata Makarantar Secondary ta 'Yan Mata. akowacce rana sukan buge kamar yara 5 ko 7 ko fiye da haka.
Rannan da Allah ya taimakeni na kama wani daga cikinsu sai nace ya kira min sarkinsu. Sarkin yazo yayi sallama muka gaisa sai na tambayeshi Don Allah menene dalilin da yasa kuka hana yaran Makarantar nan su zauna lafiya?
Sai ya gaya mun wasu dalilai masu Qarfi. Daga cikin wadanda zan iya tunawa yace min:
- Yawanci ana gina makarantun ne acikin Daji. Mu kuma aljanu dajin ne wajen zamanmu.
- Wawayen cikinmu ne suke shiga jikinsu. amma masu hankalin basu shiga jikin Dan Adam sai dai in chutar dasu akayi sosai.
- Ba'a cika koyar dasu karatun addini ba. sai dai boko yafi yawa. shi kuma karatun duniya ne. Shi yasa basu jin tsoronsu.
- Yawanci yaran basu mayar da hankali akan abinda ya kawosu. kullum sai dai zantukan soyayya, ko batsa, da sauransu.
- Yaran basu cika suturcd jikinsu sosai ba. Suna zama tsirara-tsirara saboda aganinsu kamar su kadai ne awajen. basu san mazajen Aljanu suna kallonsu ba.
- Basu damu da karanta addu'o'in shiga bandaki ba. ballantana Azkar na safe da yamma.
- Suna yawaita suruta acikin Bathroom. Kuma manyan 'yan mata kamar biyu ko uku ko fiye da haka suna shiga wanka tare. suna ganin tsaraicin Junansu. wannan ma haramun ne.
- Yadda Dan Adam yake da sha'awa, to aljanu ma suna da ita. Har ma tasu ta zarce ta Dan Adam. Do. su suna saduwa fiye da sau hamsin arana guda. Shi yasa idan wata ta nuna tsaraicinta sun gani sai suji suna sonta. Daga nan kuma zasu rika zuwa acikin barci suna saduwa da ita.
Jawabin da yayi yana nan da yawa. May be zan tura Audio recording din a ZAUREN FIQHU WHATSAPP domin 'yan uwa suji.
Amma muhimmin abu dai shine mu kiyaye wadannan abubuwan, mu rika tsawatar da yaranmu Mata (har da mazan) masu zuwa makarantun Boarding Schools.
Kuma wannan kalubale ne ga Malaman Makaranta da hukumomin makarantun kwana.