Kulob din Chelsea ya sayi dan wasan gaba na Barcelona Pedro Rodriguez a kan £21m.
Dan wasan mai shekaru 28 ya sanya hannu a kan kwantaragin shekaru hudu, kuma shi ne dan wasa na biyu da kulob din ya saya a cikin mako guda, bayan sayen dan wasan Ghana Baba Rahman.
Pedro ya ce: "Ina cike da farin cikin komawa ta wannan kulob. Ina matukar shaukin fara wasa a Chelsea, kuma na zo kulob din ne domin na rika samun nasara a dukkanin wasannin da za mu yi."
Dan wasan ya godewa kulob din da kuma masu goyon bayansa saboda damar da ya samu.
Dan wasan na kasar Spain, wanda kulob din Manchester United ya so ya saya, ya zura kwallaye 99 a wasanni 326 da ya buga tun da ya soma kwallo a shekarar 2008.
Pedro ya buga wasanni 50 na gasar cin Kofin Turai a kakar wasa ta bara, ya lashe kofin gasar sau uku, inda ya ci kwallon da suka doke United a wasan karshe na cin Kofin Turai a shekarar 2011 da kuma daukar kofin La Liga sau biyar.
Dan wasan ya buga wa Barcelona wasanni uku a bana, kuma shi ne ya zura kwallon karshe a wasan da kulob din ya tashi 5-4 da Sevilla a gasar cin Kofin Uefa Super Cup.