A yau asabar ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai ziyarci Jamhuriyar Benin inda zai gana da takwaransa Boni Yayi.
Ziyarar wani bangare ne na ci gaba da tuntubar shugabannin kasashe makwabta dangane da yadda za a shawo kan hare-haren kungiyar Boko Haram dama matsalolin tsaro da ake fama da su a mashigar tekun Guinea.
A lokacin ziyarar, ana sa ran Shugaban Najeriyar zai halarci bikin ranar samun 'yancin kan kasar da ke gudana a yau.
Shugaba Buhari zai yi amfani da wannan dama ta ziyarar kwana guda domin ganawa da wakilan al'ummar Nigeria a jamhuriyar Benin.
Shugaba Buhari ya kai irin wannan ziyara kasashen Nijar da Chadi da Amurka da kuma Kamaru a baya-bayan nan.