Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya sha alwashin yin iyakacin kokarinsa wajen ganin jami'an tsaron kasar sun kubutar da 'yan matan Chibok daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram.
Shugaban ya dauki wannan alkawalin ne a yayin ganawarsa ta farko da shugabanin masu fafutukar ganin an kubutar da 'yan matan watau Bring Back Our Girls a fadarsa da ke Abuja.
Kwannaki 450 ke nan tun bayan da 'yan Boko Haram din suka sace wadanna 'yan matan su fiye da 200 daga wata makarantar sakandare da ke garin chibok na jihar Borno.
'Yan kungiyar Bring Back Our Girls sun yi zargin cewa sau uku suna rubuta wasika ga tsohuwar gwamnatin Dr. Goodluck Jonathan amma ba su samu nasarar ganawa da shi ba.
Baya ga 'yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace, kungiyar ta kuma sace wasu karin mutane da suka hada da yara kananan a yankin arewa maso gabashin kasar.
Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 15,000 a Nigeria.