YANA SHAWARA DA SAHABBANSA
Rundunar Musulmai sun riga sun iso Filin Badar tun kafin su kafiran suyo nisa daga inda suke. Amma lokacin da Manzon Allah (saww) ya samu labarin cewa Mutanen Makkah sunyi shirin yaki sun fito domin su bada kariya ga ayarin fataucinsu, sai ya kira manyan Sahabbansa domin yin shawara dasu.
Yana gaya musu cewa: "YA KU MUTANE! HAKIKA ALLAH YAYI MIN ALKAWARIN SAMUN NASARA AKAN 'DAYA DAGA CIKIN RUNDUNONIN (MAKKAH) DIN NAN GUDA BIYU, CEWA TAKU CE. KO DAI AYARIN FATAUCINSU, KO KUMA RUNDUNAR YAQIN".
Sai wani Sahabi mai suna ALMIQDAD BN AL-ASWAD (ra) ya mike tsaye yace: "Ya Ma'aikin Allah, ka tafi izuwa ga duk abinda Allah ya umurceka dashi. Wallahi mu ba zamu gaya maka irin abinda Banu Isra'eela suka gaya ma Annabi Musa ba (as). alokacin da suka ce masa "KU TAFI DAKAI DA UBANGIJIN NAKA KUYI YAKI (DA KAFIRAI) MU MUNA ZAUNE ANAN".
Sai dai mu zamu ce maka "Kaje dakai da Da Ubangijinka kuyi Yaki, mu ma zamuyi yakin tare daku". Wallahi da zaka tafi damu zuwa BARKUL GHIMADI (wani kududdufi ne mai nisa sosai) da sai mun tafi tare dakai".
Da jin haka Sai Annabi (saww) yayi masa addu'a ta alkhairi sannan ya wajen sauran Sahabban yace musu "KU BANI SHAWARA MANA, YAKU MUTANE!". (Yana nufin yana so yaji ra'ayin Ansaar wato Sahabbansa mutanen Madeenah).
Sai Sayyiduna Sa'adu bn Mu'az (ra) shugaban Qabilar Ausu yace "Kamar mu kake nufi Ya Rasulallahi?" Sai Manzon Allah (saww) yace masa "EH HAKANE".
Sai yace "Hakika munyi imani dakai, kuma mun gaskataka, kuma mun baka alkawarinmu. Ka tafi damu kawai izuwa abinda Allah ya umurceka dashi.
Na rantse da Wanda ya aikoka da gaskiya, da ache zaka je damu bakin Tekun nan, ka keta ta cikinsa, Wallahi muma sai mun ketashi tare dakai. Bamu jin tsoron Ka hadu da abokan gaba tare damu gobe. Hakika mu zamu jure awajen Yaqi, zaka tabbatar da haka yayin da muka hadu (dasu).
La'alla Allah zai nuna maka abinda zai faranta maka ranka tare damu. Ka tafi (damu) bisa albarkar Allah".
Daga jin haka sai fuskar Manzon Allah (saww) tayi haske, yayi mutukar farin ciki da jin haka. Sannan sai yayi ma Sahabbansa albishir yace musu "KUYI FARIN CIKI, WALLAHI KAMAR GASHI NAN INA KALLON WURAREN DA ZA'A KAYAR DA MUTANEN NAN (WATO KAFIRAI).
Acikin ruwayar Imamul Bukhariy, Annabi (saww) sai da ya rika nuna wuraren da za'a kashe manyan kafiran Makkah din nan. yana cewa : "ANAN ZA'A KASHE WANE, ACHAN ZA'A KASHE WANE". yana fada yana dora hannunsa akan Qasar yana nunawa.
Daga nan sai Sahabbai suka tabbatar cewa LA BUDDA sai an gwabza yakin.
DAGA ZAUREN FIQHU
Ya Allah yi salati da tasleemi ga Ma'aikina, a sanda ya fito da komawarsa daga filin Badar. Yi salati agareshi a sanda yake shawara da sahabbansa, Yi salati agareshi alokacin da yake farin ciki da sauraronsu, Yi salati agareshi alokacin da yake yi musu albishir da samun nasara. Yi salati agareshi gwargwadon soyayyar da take tsakaninka dashi (saww) da iyalan gidansa da dukkan Sahabbansa da masoyansa.