An haifi marigayi Rabilu Musa Ibro a shekarar
1971. Ya yi karatun Firamare dinsa a Danlasan
da ke cikin karamar hukumar Warawa.
Sannan kuma ya yi Sakandare a Kwalejin
horon malamai ta Wudil (Teachers College).
Daga nan ne ya shiga aikin gidan Yari (Prison Service) a shekarar 1991. Ya yi shekara takwas
Ya na aikin Gandiroba inda ya kai matakin
insfekto, daga nan ne ya bari ya cigaba da
sana’ar wasan kwaikwayo.
Rabilu Musa Ibro ya fara sana’ar Fim a tun ya
na aji uku na makarantar sakandare. Ya na da Mata da Yara hudu ko uku akwai : Jamila, Kubra, Auta.
Daga cikin yaransa akwai: Akwai Faisal,
Jawahid, Lawiza, Abdul-Mummuni, Sannan
akwai Asma’u, Annabe, Sa’adiyya, Akwai wani
yaro kuma da ya Haifa ya sa sunan mai gidansa wato Baba Yaro. Kafin Rasuwarsa Ya bayyana Ciroki a matsayin
dan wasan hausa abokin sana’ar sa da ya fi burgeshi.
Da aka tambayi Rabilu Musa ibro dan wasan
santimental da ya fi burgeshi sai yace “ Adamu Usher, ka ga wannan, yana bani
sha’awa. Saboda ba shi da girman kai, ba zan
manta ba lokacin rasuwar kulu da Yautai, tun
daga farkon rasuwar mu na tare da su.” In ji
Ibro
Daga cikin dubunnan fina finansa ibro ya bayyana cewa ya fi son wadannan fina finai
“Akwai Kauran Mata, Kowa Ya Debo Da Zafi,
da kuma Mai Dawa.
Ibro ya bayyana ya fi son tuwon dawa a
bangaren abincinsa, fannin sutura kuma sai
yace “Na fi son yadi wanda zan shekara da shi ina gurzawa, ba in sa Shadda ba kwana biyu in
ga tana kodewa.
Da aka tambayi Marigayi Ibro a lokacin ya na
raye me ya fi bakanta masa rai a kan harkar
sana’arsa sai yace“ Ni abinda yake bata mani
rai kawai a wannan sana’a bai wuce rashin hadin kan ‘yan wasa ba.
Rabilu Musa Ibro Ya amsa kiran mahallicinsa
ya na da shekaru 43, a duniya. Allah ya
kyautata makwanci.
An dauko daga mujallar GIDAUNIYA
Allah jikanci Da Rahma Ameeeen