Watan Ramalana lokacin da Musulmai suke yin azumi daga fitowar rana zuwa faduwarta yana iya zama lokaci mafi wahala ga mutanen da ke yin wasanni - yana da wuya ka motsa jiki a lokacin da aka hana shan ruwa.
Alice Morrison da ke birnin Marrakesh ta yanke shawarar ta gwada yin azumi na kwana daya, sanna ta yi tsere a ranar.
Ta ce, "A ko da yaushe ina sha'awar yadda kawaye na musulmai suke tunkarar watan Ramalana cikin nishadi".
Azumin watan Ramalana yana daya daga cikin shika-shikan musulinci guda biyar.
"A gani na, azumi yana da wuya sosai: rashin cin abinci da kuma abu mafi muni, rashin shan ruwa a tsakanin sa'oin fitowar rana da kuma faduwar ta, wanda a nan Morocco a wannan lokacin rani, hakan na nufin sa'oi na tsakanin karfe 03:50 da karfe 19:45".
Kuma duk da haka har yanzu miliyoyin mutane a sassan duniya daban-daban suna yin shirin atisaye mai tsanani kuma har ma su yi gasa.
A Wannan shekarar sai na yanke shawarar ni ma na yi azumin na kwana daya, saboda haka sai na saka hannu domin na yi tseren watan ramalana na tsawon kilomita 12.
An yi hakan ne domin a tara masu tsere daga sassan Morocco su sha ruwa tare, su yi tsere a duhun hamada kuma su yi murna da abinci mai yawa kafin alfijir.
'Agogo mai kararrawa'
A daren, na sa kararrawa ta a karfe 3:30 domin na tashi na ci abinci kuma na sha ruwa.
Ban ci abinci mai yawa ba a lokacin, kawai biredi da cake na ci, amma na sha ruwa lita daya da wasu 'yan kwayoyi da za su sa naji karfi da rana.
Na koma na kwanta sai na tashi karfe 06:00 kamar yadda na saba sai na dauki kofin ruwa da ke kusa da gado na.
Na sha wahala da safe saboda duk sai na ji baki na ya bushe kuma numfashi na yana wari sosai duk da yawan wanke baki na da na yi. Ban ji yunwa ba amma babu shakka na ji kishin ruwa.
Da rana, na ji yunwa kuma sai na ji duk raina yana baci. Na yi ciwon kai kadan kuma sai na ji kamar zan yi rashin lafiya, kamar na fara mura.
'Barka da shan ruwa'
Da karfe 18:00, ni da wacce muke zaune a gida daya muka fara hada kayayyakin mun domin mu fita zuwa da.
Mun bi hanya mai yashi da tsaunuka.
Wannan shi ne lokacin da sau da yawa mutane suke yin wasannin a watan Ramalana kuma yanzu na gane me ya sa - lokaci ya gabato. Yanzu da ya rage sa'oi 2 a sha ruwa, ba zato ba tsammani kawai sai na ji wani karfi.
Da karfe 22:30 sai wata ya fito.
Sai muka taru a wurin da za mu fara da tocilan wanda ake daura a kai, sai muka yi wa junan mu fatan nasara da kuma "barka da Ramalana".
Mun bi hanya mai yashi da tsaunuka masu tsini a dukkanin gefen.
A wurina Ramalana ya zama jiki a lokacin - yadda mutane ke nuna da'a da kokari ba tare da wani bambancin matsayi ba wajen yin aiki daya; sannan kuma ga murna da jin dadi da ake yi.