Nigeria ta bukaci kulla alakar kud da kud da Jamus, domin ta farfado da wasan tamaula da kuma ci gaban tawagar kwallon kafarta.
Shugaban hukumar kwallon kafar Nigeria, Amanju Pinnick, ya fada a shafin intanet na hukumar cewar "Ya kagara ya kulla hulda da hukumar kwallon Jamus da kuma ta Bundesliga".
Pinnick ya kara da cewar muna fatan samun tallafi kan shirye-shiryen da za su bunkasa mana wasan kwallon kafar mata da alkalan wasan da kuma masu horas da tamaula.
Tuni aka fara tattaunawa tsakanin jami'an NFF da ambasadan Jamus na Nigeria, Dietmar Kreusel kan yadda Jamus za ta taimakawa Nigeria.
Nigeria wacce ta yi fi ce a harkar kwallon kafa a nahiyar Afirka, ta yi fama da koma baya a fagen tamaular a shekarun baya a manyan wasannin duniya.
Nigeria ta dare mataki na 10 a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a duniya a 2006, amma a yanzu tana matsayi na 57 a duniya a jerin da Fifa ta fitar a watan Yuni.