Akalla mutane 44 ne suka rasa rayukansu sannan kuma wasu 47 sun jikkata bayan tashin tagwayen bama-bami a Jos, babban birnin jihar Plateau da ke tsakiyar arewacin Najeriya, a daren Lahadi.
Daya daga cikin bama baman ya tashi a masallacin 'yan taya a lokacin da shugaban majalisar malamai na kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'a Wa Ikamatu Sunnah ta kasa, Sheik Sani Yahaya Jingir, ya ke gudanar da tafsirin karatun Al'Qur'ani, al'amarin da aka ce ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21 sannan wasu da dama sun jikkata.
An dai ce wani mutum ne ya zo masallacin a inda ya zaro bindiga ya bude wuta akan mutane kafin ya fara jefa gurneti cikin masallacin sannan kuma daga bisani bom din ya tarwatse da shi.
Kafin tashin bam din a masallacin, sai da wani ya fara tashi a gidan cin abinci da ke kan titin Bauchi Road a birnin, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 23.
Hukumar agajin gaggawa ta NEMA ta ce mutane 47 ne suka jikkata a hare-haren guda biyu.