Manyan malamai sunyi kokarin tattara, manyan laifukkuka, a guri guda domin sanin su, da fahimtar munin su, da yadda za'a guje musu.
Allah ya bamu ikon kiyayewa.
1- Shirka da kashe-kashenta
2- kisan kai
3 - Tsafi
4- Wasa da sallah
5- Hana zakka
6- Sabawa iyaye
7- Cin riba
8- Cin dukiyar marayu
9- yiwa Annabi saw karya
10- Karya Azumi da gangan
11- Gudu daga filin daga ana yakin kare addini.
12- Yin Zina
13- Shugaba mai hainci ga talakawansa.
14- Shan giya da sarrafata
15- Girman kai da takama da jiji da kai
16- Shedar Zur
17- Luwadi da mdigo
18- Yin kage ga muminai
19- Satar dukiya daga baitul mali
20- Zaluncin cin dukiyar jamaa, ta algus da manuba.
21- Sata, da sane.
22- Fashi da makami
23- Rantsuwar karya
24- Yawan karya
25- Wanda ya kashe kansa da gangan
26- Mugun Alkali,
27- Maza masu koyi da mata da Mata masu koyi
da maza
28- Masu auran kisan wuta
29- Masu cin mushe da shan jini da alhanzir
30- Rashin tsarki daga fitsari.
31- Masu karbar dukiyar Jamaa babu dalili
32- Munafinci
33- Ha'inci
34- Yin ilmi don duniya da boye ilimi mai amfani
35- Yin gori idan ka yiwa mutum wani alkhairi,.
36- Karyata kaddara
37- magulmaci
38- Mai yawan laantar mutane
39- mayaudari
40- Gasgata bokaye da yan tsibbu
41- Mace mai tsiwa ga mijinta
42- Rashin sada zumunta
43- Sassaka gumaka
44- Annamimanci
45- Kukan mutuwa (yin hawaye babu laifi)
46- Sukan Nasabar mutane, da cin mutunci.
47- Cutar Jamaa, ta kowacce fuska.
48- Kafurta mutane,babu dalilin daga sharia
49- Dunguma ashariya da yawan zage- zage.
50- Zagin waliyai da bayin Allah malamai