Lailatul Qadri dare ne Mai matukar albarka a cikin Watan Ramadhan ,shine daren da Yafi watanni dubu alfarma.
Ana Tsammanin daren Lailatul Qadri ne a Goman karshe na Watan Ramadhan, musamman an fi sa rai a Dararen wutri.
daren 19, 21, 23, 25, 27, 29.
An ruwaito Cewa, Idan Goman karshe na Ramadhan ya shigo, Manzon Allah Mai tsira da Aminci ya kan tashi da iyalansa (Da Dare), yakan Kara yawan ibada da Neman kusanci ga Allah Ta'ala ta Hanyar salloli, Azkar, da karatun al-Qur'ani.
Da aka tambayi Manzon Allah Mai tsira da Aminci Cewa,
"Me ya kamata mutum ya Roka a daren Lailatul Qadri?
Sai yace "Kuce, Ya ubangiji! Kai ne Mai afuwa, kana son afuwa, kayi mana afuwa!"
Tirmiziy ne ya ruwaito.
Ya Yan Uwa Musulmi Watan Ramadhan ya kusa wucewa, babu Wanda yake da tabbacin kaiwa wani ramadhan a cikin mu, Dan Haka mu Dage da ibada, mugayawa Allah damuwar mu da bukatun mu, Allah zai amsa da ikon sa.
Ya Allah ka bamu zaman Lafiya a kasar mu, ya Allah Allah kayi mana afuwa, lallai Kai Mai afuwa ne.
Allah ya datar da mu.