TAMBAYA TA 1647
********************
Assalamu alaikum Malam. Na haihu ne sai na yi arba'in a na gobe azumi to a daidai sanina tsawon nifas kwana arba'in ne sai na yi wanka na fara ibada Duk da bai tsaya ba, har nayi azumi hudu sai aka ce min tsawon nifas kwana sittin ne, to sai na tsaya da ibada na. to mallam don Allah wannene daidai kuma ya matsayin azumin da nayi?.kuma da ranakun da banyi azumi da sallah ba?
(Daga wata baiwar Allah)
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah.
Hakika shi jinin Nifasi, Akwai Sabanin malamai dangane da Karancin kwanakinsa da kuma Qurewar yawan kwanakinsa.
Shi dai awajen Imamuna Malik da Imam Abu Hanifah da Imam Ahmad, mafi yawan kwanakin jinin haihuwa kwana Arba'in ne. Idan jininta ya dauke koda aranar da ta haihu ne, Mace zatayi wanka taci gaba da sallah da azuminta.
Amma idan wadannan kwanaki arba'in din sukayi kuma jininta bai tsaya ba, Mace zatayi wanka taci gaba da sallarta da azuminta.
Kuma sun yi dogaro ne da wasu hadisai daga Sahabban Manzon Allah (saww) kamar haka:
Daga Sayyida Ummu Salamah (ra) matar Manzon Allah (saww) tace: "Mata masu haihuwa sun kasance azamanin Manzon Allah (saww) suna zaman kwana arba'in ne bayan haihuwar da sukayi".
- Bukhary da Muslim da Ahmad da Tirmizy da Abu Dawud ne suka ruwaito hadisin.
Awata ruwayar Imam Abu Dawud dun kuma, Ummu Salamah tace "KUMA MANZON ALLAH (SAWW) BAI TABA UMURTARSU DA RAMUKON SALLOLINSU NA LOKACIN BEEQI BA".
- Imamul Hakim ya inganta hadisin, kuma Imam Nawawiy (rah) yace amma zancen da da wasu Malaman hadisi sukayi akan wai hadisin mai rauni ne, ABUN MAYARWA NE GARESU (wato zancensu ba karbabbe bane) domin kuwa hadisin yana da wasu hadisan da suka Qara masa Qarfi.
Kamar hadisin da Ibnu Maajah ya ruwaito daga Anas bn Malik (ra) cewa "Manzon Allah (saww) ya ajiye ma masu jinin BEEQI kwanaki arba'in ne. Sai dai idan sun ga alamar tsarki kafin haka.
Sannan Imamul Hakim ya ruwaito daga Sayyiduna Uthman bn Abil-Aas (ra) yana cewa "Manzon Allah (saww) ya ajiye kwana arba'in ga mata alokacin haihuwarsu".
Imamus San'aaniy (rah) yace: "Wadannan hadisai dukkansu suna karfafan junansu ne. Kuma suna ishara ne da tabbatuwar hukuncin jinin haihuwa ga mata, kwana arba'in ne. Zata zauna ba zatayi sallah ko azumi ba.
Duk da dai wannan hadisin bai fito Qarara ya nuna hakan ba, amma wasu hadisan sun nuna. Kuma ga ruwayar Anas bn Malik ma ta nuna cewar idan mace taga tsarki kafin kwanaki arba'in din to zatayi sallah da azuminta.
Imam Tirmiziy ma yace "Dukkan Malamai ma'abotan Ilimi sun hadu akan cewa Mace mai jinin Beeki zata zauna tsawon kwana arba'in ne. (Idan bata ga tsarki ba, to ya zama jinin rashin lafiya kenan. Ba zai hana sallah ko azumi ba.).
Azuminki guda hudu da kikayi sunyi daidai. Amma zaki rama sallolinki da azuminki ba wadannan sauran kwanakin da kika zauna.
Duk da dai akwai wata ruwayar daga Imam Malik cewa kwanaki sittin ne, to amma wannan ruwayar da muka kawo tafi waccan din Qarfi saboda dogaro da wadannan hadisan masu Qarfi.
Don Qarin bayani aduba :
TALKHEES na Hafiz Ibn Hajr Juzu'i na 1, shafi na 181.
Subulus Salam na San'aaniy, juzu'i na 1 shafi na 181 zuwa 182.
WALLAHU A'ALAM.