DAKARU SUNYI SAHU SAHU
Shi dai filin da aka gwabza wannan yaki na Badar, wani waje ne mai rijiyoyi yana da nisan Kilometers 130 a kudu maso yammacin birnin Madeenah.
Yayin da rundunar Musulmai suka Qarasi suka samu wajen tsayawa acikin Kwarin na badar, sai wani Sahabi mai kaifin hankali, ana ce masa Al Hubbab bn Munzir ya duba yaga cewa sun tsaya ne daga bayan rijiyoyin badar din.
Din haka ya bama Manzon Allah (saww) shawarar cewa su koma daga gaban rijiyoyin gaba daya. Su rufe dukkan rijiyoyin wajen gaba daya, su bar guda daya rak, wacce zasu rika sha daga gareta.
Wannan dabarar tay kyau. Domin kuwa su kafiran basu da ruwan sha anasu bangaren. Gashi kuma sun ci nama, sun sha giya, suna bukatar ruwa sosai saboda Qishirwa.
Shi kuma Sa'ad bn mu'az (ra) ya bada shawarar cewa su kafa wata rumfa wacce Manzon Allah (saww) zai tsaya acikinta. Don haka sukayi masa rumfa daga saman wani tudu.
Daga nan sai Dakaru suka jeru SAHU SAHU, Shi kuma Manzon Allah (saww) ya rika shiga Tsakanin sahun yana gyarasu. Sannan ya kalli kafiran Quraishawa suma yaga sunyi sahu sahu. Sai yayu addu'a yana cewa:
"YA ALLAH GA QURAISHAWA NAN SUN FITO DA DAWAKANSU DA ALFAHARINSU, SUNA JAYAYYA DAKAI, KUMA SUNA QARYATA MANZONKA. YA UBANGIJI INA ROKONKA KA (TABBATAR MIN) DA NASARAR NAN WACCE KAYI MIN ALKWARINTA".
DAGA ZAUREN FIQHU :
Nan zamu tsaya sai a kashi na tara zamu ci gaba. kafin nan aduba cikin:
- SEERATUR RASUL na Ibnu Is'haq, juzu'i na 2 shafi na 311.
- ALBIDAYAH WAN NIHAYAH na ibnu Katheer, juzu'i na 3, shafi na 267.
- AT-TABAQAAT na Ibnu Sa'adin juzu'i na 2, shafi na 216.
DA FATAN AN SHA RUWA LAFIYA.