AN TURA 'YAN LEKEN ASIRI
Dama na riga na gaya muku cewar yayin da Abu Sufyan (Shugaban ayarin kasuwancin Mutanen Makkah) ya samu labarin cewa Manzon Allah (saww) ya fito domin tare ayarinsa, sai ya dauki hayar wani Mutum wanda zai nuna masa hanyar da zai bulle. ya kauce ma ainahin hanyar da ake zaton zai bi.
Yayin da ya samu ya tsere ta wannan hanyar sai ya aika ma kafiran Makkah yana sanar dasu tare da basu shawarar cewa su koma gida tunda gashi dukiyarsu ta tsira.
Qasurgumin kafirin nan Abu Jahal daga jin haka sai yace "A'a ba zamu koma gida ba, Har sai mun je Filin Badar mun zauna tsawon kwanaki uku, Mu yanke rakuma, muci abinci, mu sha giya. Idan sauran Qabilun Larabawa suka samu labarinmu ba zasu gushe suna jin tsoronmu ba har abada".
Shi kuwa AL-AKHNASU BN SHAREEQ ASSAQAFIY sai ya mike yace ma bangaren Mutanensa su koma gida tunda dukiyarsu ta riga ta tsira. Don haka babu koda mutum guda wanda ya halarci yakin badar daga Banu Zahrata (dangin mahaifiyar Manzon Allah saww) da kuma Banu Adiyyin.
Su kuma sauran kafiran sai suka ci gaba da tafiya har sai da suka sauka a filin Badar. Daga chan gefen kwarin.
Su kuwa Rundunar Musulmai yayin da suka kusan Qarasowa badar sai Manzon Allah (saww) ya tura mutum biyu domin leken asiri. Suje su samo labarin halin da rundunar kafirai suke ciki. Wadannan mutane biyun sune Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib da kuma 'Dan uwansa Azzubair bn Al-Awwaam (Allah shi yarda dasu).
Sun samu nasarar kamowa wasu samari guda biyu wadanda mutanen Makkah suka aikesu domin su samo musu ruwan sha. Sun kamosu suka kawosu gaban Manzon Allah (saww).
Shi kuma alokacin nan yana sallah.
Nan zamu tsaya. Sai a fitowa ta bakwai.
Asha ruwa lafiya.