ALLAH YA SAUKAR MUSU DA RUWA
Yayin da Manzon Allah (saww) ya idar da sallarsa sai ya tambayi Wadannan samarin da aka kawo gabansa "KU BANI LABARIN RUNDUNAR QURAISHAWA".
Sai suka ce "Suna bayan Tudun nan". Sai yace "NAWA NE ADADIN YAWANSU? ". Sai suka ce "Bamu sani ba". Sai yace "RAKUMA NAWA SUKE SOKEWA A KULLUM?" Sai suka ce "Wataran guda tara, wataran kuma guda goma". Sai yace "MUTANEN SUN KAI TSAKANIN MUTUM 900 ZUWA DUBU DAYA".
Sannan sai ya tambayesu sunayen wasu daga cikin mutanen da rundunar ta Qunsa. Sai suka ambato masa wani adadi mai yawa. Sai Manzo (saww) yace ma mutanensa "GA MAKKAH NAN FA TA JEFO MUKU MAFI DADIN KAYAN CIKINTA" (Wato mafiya muhimmancin mutanen cikinta kenan).
Sai suka ci gaba da tafiya har sai da suka sauka acikin kwarin Badar wanda yake bangaren gefen hanyar madeena. Nesa da wajen ruwa, kuma awani waje mai Qasar gishiri gishiri.
Sun kwana anan sai suka wayi gari mafiya yawansu suna jin Qishirwa, kuma ga wadansu sun tashi da janabah. Daga nan sai Shaitan (L. A) ya fara jefa waswasi acikin zukatan wasu sahabban yana gaya musu cewa : "Babu abinda mushrikan nan (Mutanen makkah) suke jira illa idan Qishirwa ta fasa muku makogoro, sai su kuma suzo su aikata muku abinda suka ga dama.
Amma sai dai falalar Allah da Rahamarsa tana tare dasu. Nan take sai UBANGIJI ya saukar musu da ruwan sama mai yawa har sai da ruwan ya riga gudu acikin kwarin da suke. Suka diba suka sha sukayi alwala sukayi wanka, Suka cika gorukan ruwansu, Sannan sai Qasar ta shanye ruwan. Wajen ya zama daidai yadda sawayen mutane zasu tabbata, ba zasu rika zamewa ba.
Su kuwa abangaren Mushrikan Makkah, wannan ruwan sai ya zama bala'i da musiba agaresu. Domin kuwa ya sanya Qasar wajen da suke ta chabe, wajen ya yamutse yadda babu damar su Qara matsawa.
Shi kuwa Manzon Allah (saww) sai Allah ya nuna masa adadin Mushrikan acikin mafarki ya gansu kamar 'Yan kadan. Saboda kar zukatan Muminai su karaya.
Nan zamu tsaya sai a kashi na takwas kuma in sha Allahu.