Kasar Girka kasa ce da ke nahiyar Turai wacce ta fada cikin rushewar tattalin arziki sakamakon dimbin bashi. A wani lokaci an rufe bankuna wasu kuma sannan kuma an takaita yawan kudaden da mutum zai iya fitarwa. Saboda haka sai mutane suka yi tururuwa zuwa bankuna domin kwashewa kudadensu har aka sami dogayen layika.
Mr. Giorgos Chatzifotiadis wani tsoho ne mai karban fansho ya je har bankuna hudu amma ya kasa fitar da kudinsa na fansho da ya ke ciyar da iyalansa da su. Da ya rasa yadda zai yi kawai sai ya fita bakin bankin ya zauna a kasa ya fashe da kuka.
Mutanen da ke wajen suka yi ta daukarsa a hoto suna sanyawa a facebook da sauran kafafen sada zumunta na zamani. James Koufos, wani Attajiri dan kasar Autralia ya ganshi a facebook kuma ya gane shi, tsohon abokin babansa marigayi ne da suka yi makaranta tare, nan da nan ya rubuta a shafinsa na facebook, cewa duk wadda yake da bayanai a kan wannan tsoho ya taimaka ya tuntube shi don kuwa abokin mahaifinsa ne kuma abin ya bashi takaici yai alkawarin biyansa kudin fanshonsa har na shekara guda.
A yanzu haka dai Mr. Koufos zai tashi daga kasar Australia a can kusurwar karshen duniya ya taho har kasar Girka kusan tsakiyar duniya domin taimakawa tsoho kuma abokin mahaifinsa.
Tsohon dai na karban Euro 120 ne kimanin Naira 26,000 a duk sati amma yanzu Mr. Koufos ya ce zai ke bashi Euro 250 kimanin Naira 54,000 a kowane sati har na fiye da shekara guda.
---------------------------------------
Hadisin Ma'aikin Allah ya ce, "Lallai mafificiyar da'a ita ce mutum ya sadar da zumunci wa masoyan mahaifinsa". Muslim ya ruwaitoshi daga Abdullahi Ibn Umar.
--------------------------------------
Abdullahi Ibn Umar wata rana sun hadu da wani bakauye a hanyar Makka sai ya masa sallama, ya kuma bashi jakin da yake kai ya hau, ya cire rawanin da yake kansa ya bayarwa bakauyen nan. Abdullahi Ibn Dinar ya ce, sai muka ce masa, Allah ya kyautataka, wadannan kauyawa ne in ka ba su abu kadan ma murna za su yi. Sai Abdullahi Ibn Umar ya ce, mahaifin wannan masoyin Umar ne kuma na ji ma'aikin Allah yana ce wa, "Lallai mafificiyar da'a ita ce sada zumunci shi ne mutum ya sadar da zumuncin masoyan mahaifinsa".
------------------------------------
A ganinku me ya sa ni zubar da kwalla ko kuma hawaye?