Wata kotun tarayya da ke jihar Kano ta bukaci a kai tsohon gwamnan jihar Jigawa da ke Najeriya kurkuku bayan hukumar EFCC ta gabatar da shi a gaban ta.
Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin aziki zagon ƙasar, EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan tare da 'ya'yansa biyu da kuma wani mutum a gaban kotun ranar Alhamis bayan ta kama shi ranar Talata.
EFCC ta ce ta gurfanar da Sule Lamido a gaban kuliya ne bisa zargin sama-da-faɗi da makuden kudade a lokacin mulkinsa.
A zaman kotun na ranar Alhamis, an girke jami'an tsaro a ciki da kewayen kotun, inda ba a bar kowa ya shiga cikinta ba, daga lauyoyi sai 'yan jarida da mutane kalilan.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan da 'ya'yansa sun yi cuwa-cuwar sama da N1.3 bn.
Ko da a karshen shekarar 2012 jami'an hukumar EFCC sun kama ɗaya daga cikin 'ya 'yan tsohon gwamnan, Aminu Sule yana shirin fita kasar waje da maƙuden kuɗaɗe.