Jirgin sama mai amfani da hasken rana wanda matukin jirgi dan kasar Swizlan Andre Borschberg ke tukawa ya yi tafiya mai nisa da bai taba yi ba.
Yadda jirgin ya wuce ta kan tekun Oceanic tsawon kwanaki ya kafa tarihi tare da bayar da mamaki.
Jirgin ya tashi daga kasar Japan zuwa Hawai inda ya yi tafiya mai nisan gaske wanda hakan ya sa ya kafa tarihi.
Bayan yin tafiya ta kusan kilomita dubu 7,900 jirgin ya sauka a birnin na Hawai.
Jirgin ya kasance a sama a nisan mita dubu 9 inda ya kuma yi tafiyar awanni 105 a sama ba tare da ya sakko ba.
Bayan jirgin ya kammala hutawa a Hawai, zai bar Amirka inda zai tafi zuwa Phoenix.
Jirgin dai wata babbar nasara ce a harkar kere-kere kuma yana da nauyin tan 2.3 inda fika-fikansa ke da tsayin mita 72.
Jirgin dai nada faya-fayan nadar makamashi daga rana guda dubu 17 inda yake yin tafiyar kilomita 70 a awa daya.